\ ‘Dan kasuwar da aka rufewa kamfani a Kano ya yi nasara a kan Gwamnatin Ganduje - BZGLOBALSERVICE.COM.NG ‘Dan kasuwar da aka rufewa kamfani a Kano ya yi nasara a kan Gwamnatin Ganduje - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
 • LABARAN YAU

  Tuesday, May 5, 2020

  ‘Dan kasuwar da aka rufewa kamfani a Kano ya yi nasara a kan Gwamnatin Ganduje


  Rohoton: http://hausa.legit.ng

  A ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, wata babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja ta bada umarnin cewa gwamnatin jihar Kano ta bude kamfanin casar shinkafar nan na Tiamin.

  A watan Afrilun ne gwamnatin Kano ta garkame kamfanin casar shinkafar da sunan cewa ya yi kusa da dakin da aka killace masu COVID-19, wanda hakan ya na da illa ga lafiyarsu.

  Alkali mai shari’a Okon Abang ya ba kamfanin gaskiya a wannan shari’a da aka yi jiya. Kamfanin na Tiamin Rice Producing Company ne ya kai gwamnatin Kano da jami’an tsaro kotu.

  Daga cikin wadanda kamfanin ya kai gaban alkali har da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano da kuma ma’aikatan tsaro na NSCDC. A karshe kuma kamfanin ya samu nasara a kotu.

  Lauyoyin Tiamin sun kalubalanci matakin da hukuma ta dauka na rufe kamfanin saboda kusanci da marasa lafiya. Lauyoyin sun gabatarwa kotu da tarin hujjojinsu a zaman da aka yi.

  Daga cikin hujjojin da lauyoyin kamfanin su ka bada shi ne su na cikin wadanda gwamnatin jihar Kano ta ba damar cigaba da aiki domin a samar da abinci a lokacin wannan annoba.

  Saboda ganin yadda kamfanin ke taimakawa wajen nemawa jama’a abin yi da samar da isasshen abinci a Kano, lauyoyin kamfanin su ka nemi alkali ya ruguza matakin da aka dauka.

  Alkali Abang ya jira wadanda ake tuhuma domin su zo gaban kotu su kare kansu, amma ba su yi hakan ba. Lauyoyin gwamnati da jami’an tsaron ba su iya zuwa kotu ba inji Daily Trust.

  A karshe kotu ta amince da bukatun Tiamin, ta ce a bude kamfanin shinkafar, ta ce lallai an ba wannan kamfanin damar aikin casar shinkafa domin taimakawa Bayin Allah da abinci.

  Babban kotun tarayyar ta yanke hukunci cewa rufe kamfanin ya ci karo da hakkin jama’a da dokar Najeriya ta tanada. An bukaci IGP da kwamishinan ‘yan sanda su bude kamfanin.

  KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

  KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

  KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: ‘Dan kasuwar da aka rufewa kamfani a Kano ya yi nasara a kan Gwamnatin Ganduje Rating: 5 Reviewed By: Admin