--
An kama wasu Katsinawa uku da su ka zazzagi Buhari a dandalin sada zumunta

An kama wasu Katsinawa uku da su ka zazzagi Buhari a dandalin sada zumunta



Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta sanar da kama wasu mutane uku da su ka zagi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari. An kama mutanen ne bayan wani faifan bidiyonsu da su ke zagin shugabannin ya kewaya a dandalin sada zumunta. Mutanen uku da aka kama sun hada da wani dattijo dan shekara 70 mai suna Lawal Abdullahi Izala, da Bahhajje Abu, da Hamza Abubakar, dukkansu mazauna unguwar Gafai a cikin garin Katsina.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce an karar da rundunar 'yan sanda a kan wani faifan bidiyo da wani Lawal Abdullahi, wanda aka fi sani da 'Izala', ya ke zagin Buhari da Masari a cikinsa. "A Saboda haka, kwamishinan 'yan sanda na jihar Katsina, CP Sanusi Buba, ya bayar da umarnin gudanar da bincike, wanda ya kai ga an kama mutanen uku," a cewarsa.


Ya kara da cewa, "a yayin da mu ke tuhumarsu, wadanda ake zargi sun amsa laifinsu. "Ya kamata jama'a su sani cewa rundunar 'yan sanda ba za ta nade hannayenta tana kallon wasu tsirarun marasa tarbiyya suna sabawa dokokin kasa ba.

"Duk wanda aka samu ya na amfani da dandalin sada zumunta domin zagin wani mutum ko wasu mutane, zai fuskanci fushin doka, kamar yadda aka tanada a karkashin dokokin hukunce - hukuncen manyan laifuka a yanar gizo."


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com



KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "An kama wasu Katsinawa uku da su ka zazzagi Buhari a dandalin sada zumunta "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?