\ Allahu Akbar: Babban burin Zainab a rayuwa shine tayi aure ta haihu, Allah ya karbi rayuwarta bayan tayi aure ta dauki ciki na wata 2 - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Allahu Akbar: Babban burin Zainab a rayuwa shine tayi aure ta haihu, Allah ya karbi rayuwarta bayan tayi aure ta dauki ciki na wata 2 - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
 • LABARAN YAU

  Sunday, May 17, 2020

  Allahu Akbar: Babban burin Zainab a rayuwa shine tayi aure ta haihu, Allah ya karbi rayuwarta bayan tayi aure ta dauki ciki na wata 2  Wani labari mai cike da alhini da abin tausayi na ta yawo a shafin sadarwa na Facebook
  Labarin wata baiwar Allah ne mai suna Zainab da ta koma ga Allah a cikin wannan wata mai alfarma
  Zainab na da buri guda biyu a rayuwa, Allah ya cika mata daya, sai dai kafin ta samu ganin dayan Allah ya karbi rayuwarta
  Wani labari da muka samu yana yawo a shafin sadarwa na Facebook ya nuna yadda wata baiwar Allah, da tayi aure wata uku da suka wuce ta koma ga Allah.

  Amaryar mai suna Zainab an bayyana cewa babban burinta a rayuwar nan na duniya shine tayi aure ta kuma haihu.

  Sai dai dama ance kana taka Allah yana tashi, domin kuwa bayan tayi aure da wata uku ta kuma dauki cikin wata biyu sai Allah ya karbi rayuwarta a cikin wannan wata na Ramadana.

  Wani abin mamaki da mutuwar ta din shine, ta mutu ba tare da wani ciwo ba, kawai tayi karar cikinta yana ciwo ne bayan ta kammala sahur.

  Ga dai takaitaccen labarin yadda lamarin ya kasance da aka wallafa a shafin Facebook:
  Copied Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Her desires in this world are just two and very simple ones: 1. To get...
  Posted by Key Point on Saturday, 16 May 2020

  KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


  KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

  KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Allahu Akbar: Babban burin Zainab a rayuwa shine tayi aure ta haihu, Allah ya karbi rayuwarta bayan tayi aure ta dauki ciki na wata 2 Rating: 5 Reviewed By: Admin