--
Yanzu Yanzu: Mutane 11 sun sake kamuwa da cutar COVID-19 a jahar Bauchi

Yanzu Yanzu: Mutane 11 sun sake kamuwa da cutar COVID-19 a jahar Bauchi



- An sake samun sabbin mutane 11 da suka kamu da cutar coronavirus a jahar Bauchi - A yanzu jimlar mutane 25 kenan suka kamu da cutar a jahar - Zuwa yanzu an sallami shida daga cikinsu, yayinda 19 ke dauke da cutar Rahotanni sun kawo cewa jahar Bauchi ta sake samun sabbin mutane 11 da suka kamu da cutar coronavirus, a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu. A yanzu jimlar mutane 25 kenan suka kamu da cutar a jahar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Daga cikin su an sallami mutane shida, yayinda a yanzu 19 ke dauke da cutar sannan babu wanda ya mutu a jahar. Yanzu da aka samu karin masu cutar, gwamnatin jahar Bauchi ta yi kira ga al’umma da su sanya idanu sosai domin kare kansu.

A wani labari na daban, mun ji cewa Shugaban Amurka Donald Trump, ya sake nuna yatsa zuwa ga gwamnatin kasar China, da cewa ita tayi sakacin da ya haifar da yaduwar cutar korona a duniya. Kamar yadda sashen Hausa na BBC ya ruwaito, Trump ya ce kasar China na da ikon hana yaduwar cutar zuwa sauran sassan duniya.

A hakan ne dai shugaban na Amurka ya ce tabbas sai an gudanar da gagarumin bincike domin gano matakan da gwamnatin China ta dauka tun a yayin da cutar korona ta fara bulla a kasar. Mista Trump bai gushe ba dai yana ci gaba da cewa,

kamata ya yi gwamnatin China ta dauki matakai cikin hanzari na hana annobar korona bazuwa daga tushenta. Furucin shugaba Trump ya zo ne a cikin jawaban da ya gabatar a wani taron manema labarai a makon da muke ciki. Babu shakka dai annobar coronavirus ta kashe dubban mutane a fadin duniya, tun bayan bullar bakuwar cutar mai shafar numfashi a watan Disamban da ya gabata a garin Wuhan na kasar China. Haka kuma babu tantama a baya dai Shugaba Trump ya sha kiran coronavirus ''Yar China'.



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Yanzu Yanzu: Mutane 11 sun sake kamuwa da cutar COVID-19 a jahar Bauchi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?