--
Tinubu: COVID-19 ta hallaka CSO di na, amma ni da Mai dakina mu na nan garau

Tinubu: COVID-19 ta hallaka CSO di na, amma ni da Mai dakina mu na nan garau

Fitaccen ‘dan siyasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi magana game da mutuwar Lateef Raheem. Marigayin ya kasance babban dogari na-hannun daman Bola Ahmed Tinubu. Jagoran na jam’iyyar APC mai mulki ya fitar da jawabi daga ofishinsa ne a ranar Litinin. ‘Dan siyasar ya tabbatar da cewa jami’in tsaron na sa ya mutu ne a sanadiyyar cutar Coronavirus. Bola Tinubu ya ce: “Bayan mutuwar babban jami’in tsaronmu,

Alhaji Lateef Raheem, ma’aikatan NCDC sun yi dabarar daukar jininsa domin ayi gwaji a gano ainihin cutar da ta kashe shi.” Jawabin ya kara da cewa: “A yau (Litinin) an dawo da sakamakon gwajin da aka yi, an gano ya na dauke da kwayar cutar COVID-19. An killace wani hadimi da aka samu dauke da cutar” “A matsayin rigakafi Bola Tinubu da mai dakinsa sanata Oluremi Tinubu da duk wasu hadimansu, sun yi gwajin kwayar cutar COVID-19 bayan mutuwar Alhaji Lateef Raheem, a ranar Asabar.”

“Sakamakon gwajin ya shigo da safiyar nan, sakamakon ya nuna cewa Asiwaji da Remi ba su kamu da wannan cuta ba. Amma an samu wani hadimi guda da ke dauke da COVID-19.” Tinubu ya ce: “Ana cigaba da kokarin bibiyar iyali da abokan aiki wadanda wannan mutumi ya yi hulda da su domin ayi masu gwajin cutar COVID-19 kamar yadda hukumar NCDC ta saba.”


"Asiwaju ya jaddada cewa dole ayi gaskiya da keke-da-keke wajen ganin karshen wannan cuta. Babu gidan da ya fi karfin cutar ta shiga. Ka da kamuwa da cutar ta jawo kyamatar jama’a” ‘Dan siyasar ya bayyana cewa bai kamata a rika kyamar masu dauke da wannan cuta fiye da yadda ake ganin masu zazzabin masassara ko sanyi ba. Ya ce dole sai jama’a sun hada-kai. “Al’adar karyata cutar ba za ta kai mu ko ina ba, kuma za ta yi mana babbar illa a halin da mu ke ciki. Ka da ku ji tsoron yin gwaji idan kun ji alamun cutar. Dole mu yaki wannan annoba.”


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Tinubu: COVID-19 ta hallaka CSO di na, amma ni da Mai dakina mu na nan garau "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?