LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Sojojin Iran Sun Karbi Umarnin Bude Wuta Akan Jiragen Ruwan AmurkaKwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo Janar Hussain Salami ne ya sanar da bai wa dakarun kare juyin musulunci umarnin bude wuta akan sojojin Amurka da zarar sun yi barazana ga jiragen ruwan Iran
(ABNA24.com) Manjo Janar Salami dai yana mayar da martani ne akan barazanar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na cewa; an bai wa sojojin Amurka da suke tekun Fasha umarnin su harbi kwale-kwalen Iran.

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo Janar Hussain Salami ya kara da cewa; “ Mun fada musu da babbar murya cewa mun kudiri kare tsaron kasarmu da kuma manufofinmu akan doron ruwa, don haka duk wata tsokana za a mayar mata da martani mai tsanani.”

Manjo Janar Salami ya kuma cewa; An bai wa dakarun kare juyin musulunci umarnin su harbi duk wani abu mai motsi akan ruwa na ’yan ta’addan sojojin ‘Amurka da zarar sun yi wa jiragenmu na ruwa barazana.

Kwamandan dakaruk kare juyin musuluncin na Iran ya kuma jaddda aniyar Iran ta kare manufofin kasarta da al’ummarta.KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

Post a Comment

0 Comments