--
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Shehun Bama ya rasu yana da shekaru 63 a duniya

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Shehun Bama ya rasu yana da shekaru 63 a duniya



Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Allah Ya yi ma mai martaba Shehun Bama, Alhaji Kyari Ibn Umar El-Kanemi rasuwa a ranar Litinin, 27 ga watan Afrilu, ranar azumin Ramadana na 4. Daily Trust ta ruwaito gwamnatin jahar Borno ce ta tabbatar da mutuwar basaraken mai daraja na daya a jerin masarautun jahar Borno, inda tace ya rasu ne a wani asibiti dake Maiduguri.

Marigayi Kyari shi ne Shehun tsohuwa masarautar Dikwa na 7, wanda ya hada da kananan hukumomin Bama, Dikwa, Ngala da Kala-Balge.

A shekarar 2010 ne gwamnatin jahar Borno ta raba masarautar gida biyu zuwa Bama da Dikwa, kuma ta baiwa kowannensu Sarki mai daraja na daya. Kwamishinan watsa labaru da al’adun gargajiya na jahar, Babakura Abba Jato ne ya sanar da rasuwar basaraken yayin da yake jawabi game da halin da ake ciki a jahar game da COVID-19.

Jato ya ce Shehu ya dade yana fama da rashin lafiya a sanadiyyar tsufa, amma yace fadar masarautar Bama za ta sanar da shirin jana’izarsa da kuma lokacin da za’a masa sallar. Haka zalika hakimin Nganzai, Bakaka Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Elkanami ya tabbatar da mutuwar shehun inda yace: “Shehun ya rasu ne jim kadan bayan sallar la’asar a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.”


Inji shi. A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Kano ta bakin kwamishina Muhammad Garba ta ce ta gano dalilan da suka kawo mace macen da aka dinga samu a jahar a makon da ta gabata. A cewar gwamnatin jahar, mace macen na da alaka da cututtukan hawan jini, ciwon siga, sankarau da kuma cutar zazzabib cizon sauro da suka dade suna addabar jama’an jahar. Garba yace sun gano haka ne bayan sun gudanar da cikakken bincike game da mace mace, don haka yace mace macen basu da alaka da Coronavirus, saboda haka kada jama’a su firgita.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Shehun Bama ya rasu yana da shekaru 63 a duniya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?