\ Cikin daren ranar litinin: Sabbin mutane 64 sun kamu da Coronavirus a najeriya - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Cikin daren ranar litinin: Sabbin mutane 64 sun kamu da Coronavirus a najeriya - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
 • LABARAN YAU

  Tuesday, April 28, 2020

  Cikin daren ranar litinin: Sabbin mutane 64 sun kamu da Coronavirus a najeriya

  Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya watau NCDC ta sanar da samun karin mutane 64 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Litinin, 27 ga Afrilu, 2020. Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace:

  “An samu karin mutane sittin da hudu (64) sun kamu da #COVID19" 34-Lagos 15-FCT 11-Borno 2-Taraba 2-Gombe A daidai karfe 11:20 na daren 27 ga Afrilu, an tabbatar da mutane 1,337 suka kamu da cutar COIVD-19 a Najeriya Adadin wadanda aka sallama: 255 Adadin wadanda suka wafati: 40

  A wani labarin daban, Jami'an tsaro tare da hadin gwuiwar jami'an gwamnatin Kaduna sun kama wasu manyan motocin dakon kayan abinci da aka boye mutane a cikinsu. An kama motocin ne ranar Litinin a kauyen Sabon Gida da ke yankin karamar hukumar Ikara yayin da suke kokarin shiga jihar Kaduna.

  Manyan motocin sun yi yunkurin shiga jihar Kaduna ne ta iyakarta da karamar hukumar Kiru ta jihar Kano. Motocin sun yi basaja a zuwan sun dauko kayan abinci ne da zasu kai jihar Kaduna. Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar Kaduna, ya ce jami'an tsaro sun kama motocin yayin da suke rangadin tabbatar da dokar hana zirga-zirga.


  KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


  KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

  KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Cikin daren ranar litinin: Sabbin mutane 64 sun kamu da Coronavirus a najeriya Rating: 5 Reviewed By: Admin