--
Boko Haram: An sake jaddada wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Chadi

Boko Haram: An sake jaddada wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Chadi

- Kasar Najeriya da jamhuriyar Chadi a ranar Alhamis sun amince da jaddada yarjejeniyar yakar Boko Haram da ke tsakaninsu - Manjo janar Bashir Magashi mai murabus, ya sanar da hakan ne a taron da aka yi tsakanin hukumomin kasashen biyu a Abuja

- Ministan tsaro na kasar Chadi, Mahamat Aba-Ali Soilah ya yi alkawarin bada goyon baya a kan wannan lamarin Kasar Najeriya da jamhuriyar Chadi a ranar Alhamis sun amince da jaddada yarjejeniyar yakar Boko Haram da ke tsakaninsu. Ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi mai murabus ya sanar da hakan ne a taron da aka yi tsakanin hukumomin kasashen biyu a Abuja.

Ya ce yana farin cikin jaddada yarjejeniyar da ke tsakaninsu don ci gaba da tabbatar da nasarar jami'an tsaron hadin guiwa. Ya ce kirkirar MNJTF da kasashen suka yi ya kawo babbar nasara wajen yaki da ta'addanci. Ya ce akwai bukatar su jaddada yarjejeniyar.


Akwai bukatar mu nemi sabbin hanyoyin kawo karshen Boko Haram kuma wannan taron zai samar da amintattaun hanyoyin fatattakar ta'addancin. "Muna bukatar sabbin tsare-tsare wajen kawo karshen ta'addanci in har muna son yankunanmu su zauna lafiya," yace. Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, mayakan Boko Haram din sun addabi yankin Arewa maso gabas din ne tun 2009. Daga bisani ne suka tsallaka kasashen Nijar, Chadi da Kamaru, wanda ya jawo gaggawar daukar mataki. Ministan ya ce duk da nasarorin da aka samu wajen yakar ta'addancin,

Najeriya ta matukar damuwa da yadda 'yan ta'addan ke ci gaba da kaiwa dakarunta hari. Ya kara da nuna alhinin yadda garkuwa da mutane, dabanci da sauran miyagun ayyuka suka yawaita a kasar nan. Ya kara da cewa, rundunar sojin kasar nan, ba su sassauta ba wajen kokarin yakar duk wata kungiyar ta'addanci da ke yankin. Magashi ya ce babban kalubalen da duniya ke fuskanta a yanzu shine annobar coronavirus. Ministan tsaro na kasar Chadi, Mahamat Aba-Ali Soilah ya yi alkawarin bada goyon baya a kan wannan lamarin. Ya kara da cewa gwamnatin Chadi za ta rike wannan yarjejeniyar.


KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Boko Haram: An sake jaddada wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Chadi "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?