LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Annobar covid-19 ta harbi sabbin mutane 195 a Najeriya, 38 a Kano



Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da cewa karin sabbin mutane 195 ne aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya. A cikin sanarwar da NCDC ta fitar bayan 12:00 na dare a shafinta na tuwita, t

a fitar da jerin jihohi da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a kowacce jiha kamar haka; 80-Lagos 38-Kano 15-Ogun 15-Bauchi 11-Borno 10-Gombe 9-Sokoto 5-Edo 5-Jigawa 2-Zamfara 1-Rivers 1-Enugu 1-Delta 1-FCT 1-Nasarawa


NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:50 na daren ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, akwai jimillar mutane 1532 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya. An sallami mutane 255 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 44.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, an bayyana cewa tawagar kwarrarun ma'aikatan Lafiya 15 da suka zo Najeriya daga China domin taimakawa kasar wurin yaki da COVID-19 basa dauke da kwayar cutar. Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ne ya fadi hakan yayin taron da kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa kan yaki da COVID-19 ya gudanar ranar Talata. Enahire ya ce sakamakon gwajin da aka yi ya nuna dukkan yan kasar na China ba su dauke da kwayar cutar. Wannan na zuwa ne bayan sun kwashe kwanaki 14 a killace domin tabbatar da cewa ba su kamu da cutar ba.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

Post a Comment

0 Comments