--
An samu kwayar cutar covid-19 a jikin almajirai 5 da jihar Kano ta mayar Kaduna

An samu kwayar cutar covid-19 a jikin almajirai 5 da jihar Kano ta mayar Kaduna



Gwamnatin Kaduna ta sanar da cewa an samu kwayar cutar covid-19 a jikin wasu almajirai biyar da gwamnatin jihar Kano ta mayar jihar. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinar lafiya ta jihar Kaduna, Dakta Amina Mohammed-Baloni. A cewar sanarwar, wacce gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya wallafa a shafinsa na tuwita,

kwamishinar ta bayyana cewa adadin ma su dauke da cutar covid-19 a jihar Kaduna ya koma mutane 9. Dakta Baloni ta bayyana cewa an mayar da almajiran zuwa cibiyar duba cututtuka ma su yaduwa, wacce ke zaman cibiyar killacewa ta jihar Kaduna. Kazalika, ta sanar da cewa ana duba lafiyar almajiran kamar yadda ake duba lafiyar duk wanda aka tabbatar yana dauke da kwayar cutar.

Ta bayyana cewa an killace sauran almajiran da ake zargin zasu iya harbuwa daga abokansu da aka samu da kwayar cutar, kuma ma'aikatan lafiya na cigaba da sa-ido a kansu.

Yanzu haka akwai kwararan cibiyoyin gwaji guda biyu a jihar Kaduna; daya a garin Kaduna, daya a Zaria.



 Bayan barkewar annobar cutar covid a Kano, gwamnatin jihar ta yanke shawarar mayar da almajirai zuwa jihohinsu na asali. Jihar Jigawa da Kaduna na daga cikin jihohin da gwamnatin Kano ta mayarwa almajirai ma su yawa. Kwamishinar ta sake yin kira ga jama'ar jihar Kaduna a kan bukatar su cigaba da biyayya ga matakan kare kai da dakile yaduwar kwayar cutar covid-19. Kazalika, ta yi kira ga jama'a da su bawa tsafta muhimmanci, sannan suke yawan wanke hannayensu da sabulu.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "An samu kwayar cutar covid-19 a jikin almajirai 5 da jihar Kano ta mayar Kaduna"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?