--
An sake yin rashin babban malamin jami'a a Kano

An sake yin rashin babban malamin jami'a a Kano

Annobar yawaitar mace - macen jama'a a jihar Kano na cigaba da saka tsoro a zukatan jama'a, musamman a cikin birnin Kano. Legit.ng Hausa ta samu labarin mutuwar Dakta Ghali Umar na sashen koyar da ilimin zanen taswirar gidaje a jami'ar kimiyya da fasaha ta Kano (KUST) da ke Wudil. A wata sanarwa da Farfesa Shehu Musa,

shugaban jami'ar KUST ya fitar, ya ce, "mu na masu bakin cikin sanar da mutuwar Dakta Ghali Kabir Umar na bangren ilimin zane (Architecture) "Har lokacin mutuwarsa, Ghali ya kasance shugaba sannan babban malami a sashen koyar da zanen taswirar gidaje a KUST, Wudil." Farfesa Musa ya yi addu'ar Allah ya ji kansa tare da yafe kura-kuransa da yi masa sakayya da gidan Jannatul Firdaus.

Marigayi Dakta Umar ya zama mutum na 5 a cikin masu ilimi da suka mutu a Kano a cikin sa'a 72 da suka gabata. Kafin sanar da mutuwar Dakta Umar, Legit.ng ta wallaffa cewa Sheikh Tijjani Yola, daya daga cikin limaman babban Masallacin Murtala, ya mutu da safiyar ranar Talata.

An shiga sati na biyu kenan da rahotanni ke sanar da mutuwar fitattun mutane, yawancinsu dattijai, a garin Kano.

Wata majiya mai kusanci da marigayin ta sanar da jaridar 'TheCable' cewa Sheikh Yola ya mutu ne da safiyar ranar Talata a gidansa da ke karamar hukumar Gwale a cikin birnin Kano. "Ya mutu ne a gidansa da ke unguwar Gwale a cikin birnin Kano da safiyar yau (Talata), kuma an binne shi da misalin karfe 9:00 na safe,"

a cewar majiyar. Wani mazaunin Kano mai suna Abdullahi Umar ya tabbatar da mutuwar babban malamin, inda ya bayyana cewa jama'ar birnin Kano suna cikin damuwa. TheCable ta rawaito cewa Uba Adamu, mahaifin Farfesa Abdallah Adamu, shugaban jami'ar NOUN,

ya mutu da safiyar ranar Talata. Adamu Sarawa, tsohon shugaban majlisar dokokin jihar Jigawa, ya mutu a daren ranar Litinin a gidansa da ke Kano. Kazalika, annobar mutuwar ta dauki ran Halimatu Shittu, tsohuwar shugabar wata kungiyar mata Musulmi a Najeriya (FOMWAN) reshen jihar Kano.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "An sake yin rashin babban malamin jami'a a Kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?