--
Yanda Hukumar yaki da rashawa EFCC ta gurfanar da Saraki a kotu Yau

Yanda Hukumar yaki da rashawa EFCC ta gurfanar da Saraki a kotu Yau

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da Ope Saraki, dan-uwan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a kotu. EFCC ta gurfanar da Saraki ne kan zargin tafka kudi fiye da kudin aikin kwangiloli biyu da aka bashi lokacin da yake mai baiwa gwamnan jihar Kwara shawara. 

A bangare guda, Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya bukaci babban kotun tarayya da ke Legas ta yi fatali da bukatar da hukumar EFCC ta kawo gabanta. Dr. Bukola Saraki ya bukaci kotu ta yi watsi da karar da EFCC ta kawo inda ta ke bukatar a karbe gidansa da ke Garin Ilorin a jihar Kwara, a mikawa gwamnatin tarayya. Bukola Saraki ya fadawa kotu cewa bai kamata ta yi amfani da jita-jitar jama’a da ke cewa an gina wadannan gidaje da dukiyar haramun wajen karbe masa dukiyarsa ba.

Lauyan da ya ke tsayawa Abubakar Bukola Saraki watau Kehinde Ogunwumiju SAN, ya roki kotu ta bukaci Jami'an EFCC su kawo hujjar da ke gaskata zargin da ta ke yi. Babban Lauyan Bukola Saraki Kehinde Ogunwumiju, ya bayyana cewa akwai bukatar hukumar EFCC ta fito da hujja mai gamsarwa kafin a damka mata gidajen har abada. Lauyan da ke kare tsohon gwamnan Kwara, 

ya fadawa Alkali mai shari’a Rilwan Aikawa cewa EFCC ba su kawo wata hujjar da za ta sa a mallaka masu gidajen ba. A Dismaban 2019, EFCC ta samu iznin kotu na karbe wasu gidajen Bukola Saraki da ke Unguwar GRA a Garin Ilorin, da zargin cewa da kudin sata aka gina gidajen.

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Yanda Hukumar yaki da rashawa EFCC ta gurfanar da Saraki a kotu Yau"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?