--
Sanatoci sun kirkiro sabon karancin matakin ilimi na neman shugaban kasa

Sanatoci sun kirkiro sabon karancin matakin ilimi na neman shugaban kasa

Majalisar dattawan Najeriya ta kammala karatu na biyu a kwaskwarimar da take yi ma kundin tsarin mulkin Najeriya inda ta bayyana babbar difloma ko makamanciyarta watau digiri a matsayin karancin karatun da dan takarar shugaban kasa zai mallaka kafin ya tsaya takara.

Jaridar Punch ta ruwaito wannan kudurin doka wanda Sanatan jam’iyyar PDP daga jahar Filato, Sanata Istifanus Gyang ya gabatar gaban majalisar, ya kunshi har da masu muradin tsayawa takarar gwamna a Najeriya.

Yayin da kudurin ta tanadi digiri ko babbar difloma, HND ga masu takarar gwamna da shugaban kasa, ta sanya karamar difloma, watau ND a matsayin karancin shaidar karatu da ake bukata masu neman takarar majalisar dokokin tarayya da majalisar dokokin jahohi ya mallaka.

Sai dai tanadin dokar yadda take a yanzu ta bayyana cewa: “Ya cancanci mutum ya tsaya takarar shugaban kasa idan har ya kai matakin ilimin sakandari ko makamancinsa.” Amma a yanzu an sauya sashin zuwa: “Idan har ya kai matakin ilimi na babbar difloma ko digiri.”

Bayan tsallake karatu na biyu a majalisar, sai shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya mika kudurin dokar ga kwamitin dake kula da kwaskwarimar kundin tsarin mulkin Najeriya.

A wani labarin kuma, fitaccen attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa gwamnatocin Najeriya na baya da na yanzu basa tabuka wani abin a zo gani wajen ciyar da tattalin arzikin Najeriya gaba, hakan yasa tattalin arzikin baya cigaba.

Dangote ya bayyana haka ne yayin wani taro da gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ya shirya a babban birnin tarayya Abuja, inda yace kokarin da gwamnatin Buhari ken a karkatar da akalar tattalin arzikin Najeriya daga man fetir ya yi kadan.


“Na yi kukar zuci kwarai da gaske lokacin da karanta cewa wai hukumar kwastam ta tara naira tiriliyan 1.35 a shekarar data gabata, hakan ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya baya aiki, saboda idan da yana aiki kamata ya yi a ce hukumar tattara haraji ta kasa, FIRS, ce za ta amshi wadannan kudade.” Inji shi.

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Sanatoci sun kirkiro sabon karancin matakin ilimi na neman shugaban kasa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?