Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com "Colour"
 • LABARAN YAU

  Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki,

  ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________
  Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views

  Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Monday, March 9, 2020

  Mutuwa riga: Dan kwallon Najeriya ya mutu yayin da yake tsaka da taka leda


  Dan kwallon Najeriya, Chineme Martins dake tsaron gida a kungiyar kwallon kafa ta Nassarawa United ya yanke jiki ya fadi, daga nan ya sheka barzahu a yayin da yake tsaka da taka leda. Jaridar Daily Trust ta ruwaito dan kwallon ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da kungiyarsa ta Nassarawa United ke karawa da kungiyar Katsina United, a filin wasa na Lafia dake jahar Nassarawa a ranar Lahadi, 8 ga watan Maris.

  Mutuwa riga: Dan kwallon Najeriya ya mutu yayin da yake tsaka da taka leda Source: Facebook Majiyar Legit.ng ta ruwaito Chineme ya yanke jiki ne a cikin fili bayan an dawo hutun rabin lokaci yayin da kungiyarsa Nassarawa United ke jan ragamar wasan da ci 2-0, koda ya fadi, an yi gaggawar garzayawa da shi zuwa asibitin Dalhatu Arab, inda a can aka tabbatar da mutuwarsa. 

  Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa ya halarci kallon wasan a filin wasa dake Lafiya, ya kara da cewa: “Dan kwallon yana tsaye ne shi kadai a filin wasa jim kadan bayan dawo hutun rabin lokaci da misalin minti na 47. “An baiwa kungiyarsa bugun tazara ne a lokacin, don haka yana tsaye a baya inda yake tsaron gida, kwatsam sai muka gan shi a kasa warwas, nan da nan aka sanar da Alkalin wasa, daga nan aka mika shi zuwa asibiti.” 

  Inji shi. Ita ma hukumar shirya gasar firimiya ta Najeriya, ta tabbatar da mutuwar Chineme, kuma ta yi alkawarin ganin an gudanar da bincike a kan gawarsa domin tabbatar da musabbabin mutuwar tasa. “Muna fatan sakamakon binciken da za mu gudanar zai bamu haske game da matakin da ya kamata mu dauka a gaba idan har bamu da tsarin a yanzu.” 

  Inji ta. Haka zalika hukumar ta ce za ta cigaba da tuntubar kungiyar kwallon kafa ta Nassarawa United tare da iyalan mamacin don sanin hanyoyin da suka fi dacewa su basu tallafi da gudunmuwa a wannan lokaci da suke jimami da alhini.


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Mutuwa riga: Dan kwallon Najeriya ya mutu yayin da yake tsaka da taka leda Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI