--
An tura fasto gidan yari saboda karyata cutar coronavirus

An tura fasto gidan yari saboda karyata cutar coronavirus

Hukumomi a kasar Uganda sun damke tare da tura wani fasto gidan yari bayan ya musanta wanzuwar cutar coronavirus a nahiyar Afirka. Babban faston mai suna Augustine Yiga, an zargesa ne da sanar da mabiyansa cewa babu wata coronavirus a Uganda da nahiyar Afirka.

"Fasto Yiga na cocin Revival Christian an gurfanar dashi tare da tura shi gidan yari sakamakon yunkurin assasa yaduwar muguwar cutar coronavirus a kasar," mai magana da yawun 'yan sandan kasar Uganda, Patrick Onyango ya sanar. "Ikirarin cewa babu coronavirus a Afirka da Uganda na nuna zagon kasa ga kokarin gwamnati na yakar cutar tare da hurewa jama'a kunne don su samu cutar,"

ya kara da cewa. Amma kuma lauyan faston mai suna Wilberforce Kayiwa, ya ce Yiga ya musanta zarginsa da aka yi da kokarin yada kwayar cutar. A halin yanzu an yankewa faston shekaru 7 a gidan yari.

Yiga, wanda ya mallaki gidan talabijin da rediyon don wa'azi, yana da mutane masu yawa da ke binsa kuma kwararre ne a wajen akidu mabanbanta da ikirarin manzonci.

A halin yanzu dai, kasar Uganda na da mutane 33 da suka kamu da cutar. Shugaban kasa Yoweri Museveni yayi kira ga jama'a da su zauna a gida amma kuma bai rufe kasar ba. Tun wata daya da ya gabata aka rufe makarantu, wuraren nishadi, wuraren bauta da kuma kasuwanni. An hana jama'a hawa abun hawa na haya tare da zuba mutane fiye da uku a motar gida.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "An tura fasto gidan yari saboda karyata cutar coronavirus "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?