LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Ministan Sadarwa na Nijeriya Shekh Isa Ali Pantami ya fito da sabon tsarin mallakar layin wayar selula da ake amfani da shi a yanzu.

Ministan Sadarwa na Nijeriya Shekh Isa Ali Pantami ya fito da sabon tsarin mallakar layin wayar selula da ake amfani da shi a yanzu.
------------------------------

sabuwar dokar da Ma’aikatar Sadarwa ta gindaya, wadanda suka hada da:

1. A rika yin rajista bisa Dokar Sadarwa ta 2003, mai lamba 25, Sashe na 25.

2. Duk wanda zai yi rajistar sabon layi, tilas sai ya bada lambar Shaidar Katin dan Kasa (NIN).

3. Duk wani dan kasar waje da ya shigo Najeriya, idan zai mallaki layin waya, tilas sai ya hada da lambar fasfo da ta biza din sa.

4. Sai nan da ranar 1 Ga Disamba za a kulle uzurin rashin yin wannan rajista.

5. Ba a yarda mutum daya ya mallaki layukan waya fiye da uku ba.

6. Duk lambar da jami’an tsaro suka tabbatar da an taba aikata laifi da ita, to za a kulle ta.

Ko kuna Goyon bayan wannan Sabon tsarin?

Post a comment

0 Comments