--
An sami kudi naira miliyan 324 a asusun bankin mabaraciya

An sami kudi naira miliyan 324 a asusun bankin mabaraciya

Tausayi da kirki irin na al'ummar kasa Lebanon ya saka wata mabaraciya ta zama hamshakiyar mai kudi, kamar dai yadda manema labarai suka fitar rahoton a kasar.
Hotunan mabaraciyar mai suna Wafaa Mohammed Awad dana katin kudi na bankin ajiyarta sun karade da yawa daga cikin shafukan sada zumunta na zamani bayan an bayyana cewa mabaraciyar wacce take yin bara a birnin Saida na kasar ta Lebanon ta tara kudi kimanin dalar amurka dubu dari tara, wato kimanin naira miliyan dari uku da ashirin da hudu a kudin Najeriya.

An bayyana cewa matar wacce take ajiye kudin nata a bankin Jamal Trust Bank, za ta samu kudi kimanin fam biliyan daya da miliyan dari biyu da hamsin idan aka canja kudin zuwa kudin kasar ta Lebanon.

Wannan lamari na matar ya fito fili ne bayan mabaraciyar ta yi kokarin cire kudinta duka daga bankin da take ajiye kudin zuwa wani banki saboda matsalar kudi da bankin nata yake samu.

Hoton katin da take cire kudi dashi a banki wanda ta sanyawa hannu a ranar 10 ga watan Satumba ya karade ko ina a kafafen sadarwa. Wannan ne yake nuni da cewa Awad tafi mutane da yawa da suke bata sadaka arziki.

0 Response to "An sami kudi naira miliyan 324 a asusun bankin mabaraciya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?