--
'Yan Boko Haram Sun Yi Awon Gaba Da Milyoyin Kudaden Da Aka Ware Domin Biyan Sojoji Alawus Dinsu

'Yan Boko Haram Sun Yi Awon Gaba Da Milyoyin Kudaden Da Aka Ware Domin Biyan Sojoji Alawus Dinsu

'Yan Boko Haram sun kwaci makudan kudi da wasu kayyayakin amfani daga hannun dakarun sojin Nijeriya bayan sun kai wa tawagar sojojin hari da safiyar ranar Juma'ar da ta gabata, kamar yadda majiyarmu ta 'Premium Times' ta rawaito. 

Kazalika, jaridar ta rawaito cewa wani soja guda daya ya samu rauni sakamakon harin. Mayakan sun kai wa tawagar sojojin atisayen 'Ofireshon Lafiya Dole' harin ne yayin da suke kan hanyarsu ta kai wasu kaya da kudi zuwa Biu a jihar Borno daga Damaturun jihar Yobe.

 Tawagar sojojin ta fada tarkon mayakan kungiyar Boko Haram din ne a tsakanin Azare-Kamuya da misalin karfe 9:00 na safiyar ranar Juma'a, kamar yadda majiyar soji ta sanar da Premium Times.

An yi kazamin musayar wuta tsakanin sojojin da mayakan kungiyar Boko Haram, lamarin da ya yi sanadiyar raunata soja guda daya tare da lalata kayayyakin da sojojin suka dauko da yin awon gaba da wata motar yaki mallakar bataliyar soji ta 231. Kazalika, mayakan sun yi awon gaba da zunzurutun kudi N15,492,000 da za a biya sojojin dake filin yaki alawus dinsu. Adadin kudin zai isa a biya alawus din dakarun soji 20,000 na tsawon sati guda. Ana bawa kowanne soja alawus din N1,000 kowacce rana.

Wata tawagar sojoji daga Damaturu da aka turo domin kawo wa tawagar farko agaji ta kashe dan kungiyar Boko Haram guda daya. Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa, AFP, ya rawaito cewa mayakan kungigar Boko Haram sun yi ikirarin cewa sun kashe dakarun soji guda biyu yayin harin.

Sai dai, majiyar rundunar soji ta fada wa Premium Times cewa an kashe mayakin kungiyar Boko Haram guda daya yayin da soja guda daya ya samu rauni a harin na safiyar ranar Juma'a.

0 Response to "'Yan Boko Haram Sun Yi Awon Gaba Da Milyoyin Kudaden Da Aka Ware Domin Biyan Sojoji Alawus Dinsu"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?