--
Shekaru Uku A Gidan Yari Bisa Shigo Da Buhu Daya Na Shinkafa Najeriya--Hukumar Costom

Shekaru Uku A Gidan Yari Bisa Shigo Da Buhu Daya Na Shinkafa Najeriya--Hukumar Costom

Hukumar Kwatam Dake Najeriya Tace Duk Wanda Aka Kama Da Fasa Kaurin Shigo Da Shinkafa Najeriya, To Hukuncin Zaman Gidan Kurkuku Ne Akansa Na Tsawon Shekaru Uku. 
Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam Na Kasa Col. Hameed Ali Ne Ya Bayyana Haka, Yayin Da Yake Bayyana Iyakokin Al'ummar Nigeria Da Niger A Karamar Hukumar Maigatari Dake Jihar Jigawa A Jiya Alhamis. Yace Shigo Da Kayan Abinci Najeriya Ta Barauniyar Hanya Yana Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Karya Tattalin Arzikin Najeriya. 

"Gwamantin Tarayya Tana Kokari Wajen Bunkasa Harkokin Noma, Musamman Noman Shinkafa, Amma Shinkafar Kasar Waje Ana Shigo Da Ita Kasa Ta Haramtacciyar Hanya Yana Barnatar Da Manufofin Gwamanti. Mafi Yawan Wannan Shinkafar Ana Shigo Muku Da Ita A Babura Ta Barauniyar Hanya Ne." ~ Inji Shi

"Babu Wata Matsaya, Duk Wanda Muka Kama Saimun Gurfanar Dashi Gaban Shari'a, Kuma Mafi Karancin Hukuncin Akan Fasakaurin Shigo Da Shinkafa Buhu Guda, Shine Hukuncin Zaman Gidan Kurkuku Na Shekaru Uku." ~ Inji Hamid Ali

Daga Karshe Hamid Ali Ya Roki Mutane Mazauna Kusa Da Bakin Boda Akan Su Bawa Gwamanti Hadin Kai Wajen Sanar Da Wasu Shigowa Da Kayan Abinci Ta Barauniyar Hanya Cikin Kasar Nan, Su Sanar Da Hukumomin Tsaro Wani Bayani Mai Amfani.

0 Response to "Shekaru Uku A Gidan Yari Bisa Shigo Da Buhu Daya Na Shinkafa Najeriya--Hukumar Costom"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?