--
SHARI'AR ZAƁEN GWAMNAN KANO    JAM'IYYAR PDP DA ABBA GIDA-GIDA SUN GAZA WAJEN GABATAR DA INGANTATTUN HUJJOJI A KOTU

SHARI'AR ZAƁEN GWAMNAN KANO JAM'IYYAR PDP DA ABBA GIDA-GIDA SUN GAZA WAJEN GABATAR DA INGANTATTUN HUJJOJI A KOTU

Ta faru ta na kuma daf! Da ƙarewa, domin kuwa yanzu haka kotun da ke sauraren ƙararrakin zaɓen gwamna a Jihar Kano, ta kammala sauraro da tattara bayanai da hujjojin ɓangaren masu ƙara, (jam'iyyar PDP) da ɗan takararta na gwamna, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) da kuma ɓangaren da aka yi ƙara, jam'iyyar (APC) da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Mai shari'a Halima S. Ibrahim ita ce ta jagoranci tawagar alƙalan da su ka zauna kan shari'ar, ta kuma bayyana cewa nan gaba kaɗan za a sanya ranar da kotun za ta yanke hukunci.

Shi dai lauyan jam'iyyar (APC) Alex Inzinyon (SAN) ya bayyana cewa, "jam'iyyar PDP ta yi zargin tafka maguɗi ne, amma kuma ta gaza gabatar wa kotu sahihan hujjojin da ta dogara da su wajen shigar da wannan ƙara.

A ya yin kuma da lauyan jam'iyyar ta (PDP), Abba Kanu Agabi (SAN) ya bayyana cewa sun yi imani Abba Kabir ne ya lashe zaɓe a zagayen farko, kuma wannan ita ce babbar hujjarsu.
Sai dai kuma, lauyan hukumar (INEC), Ahmad Raji (SAN), ya bayyana cewa duk wata dama da jam'iyyar (PDP) da Abba Kabir su ka nemi a ba su wajen bincike an ba su, amma duk da haka sun gaza wajen bayar da gamsassun hujjojin da za su gaskata iƙirarin da su ke a kotu. Da wannan ne ma ya buƙaci kotun da ta yi watsi gami da fatali da wannan ƙara gaba ɗaya.

0 Response to "SHARI'AR ZAƁEN GWAMNAN KANO JAM'IYYAR PDP DA ABBA GIDA-GIDA SUN GAZA WAJEN GABATAR DA INGANTATTUN HUJJOJI A KOTU"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?