--
RIKICIN IRAN DA AMURKA---- AMURKA NA CIKIN FIRGICI SAKAMAKON JAWABIN SHUGABAN RUNDUNAR SOJAN IRAN AKAN QASAR ISLARA''ILA SHIGA DOMIN KARANTAWA

RIKICIN IRAN DA AMURKA---- AMURKA NA CIKIN FIRGICI SAKAMAKON JAWABIN SHUGABAN RUNDUNAR SOJAN IRAN AKAN QASAR ISLARA''ILA SHIGA DOMIN KARANTAWA

DAGA NASIR ISAH ALI


Shugaban rundunar sojan kasar Iran.
Manjo Janar Abdorrahman Mousavi.


Ina tabbatar muku da cewar Israila tana dab da yin takunta na karshe,domin yanzu haka mun riga mun ci karfinta,don haka nan gaba kadan duk zaku shedi rugujewarta a zahiri.
Janar din yana jawabi ne a garin Qum,Janar Mousavi ya bayyana cewar,gungun masu Gwagwarmaya sun ci karfin Amurka da muradunta da yan kanzaginta a yankin gabas ta gaskiya,wanda kuma hakan ne ke yin nuni da cewar,basu da wani karsashin da zasu iya bai wa Israila wata kariya.





Yace kowa zai shedi rugujewar wannan masifaffiyar kasa wacce aka kirkireta domin zalinci da keta,kuma kar ku dauka cewar kwanukan rugujewar tata da nisa, a'a nan gaba ne kadan. Tun lokacin da aka kirkiri Israila,babu abin da take yi wanda ya wuce,mamaya,babakere,Sace-sace,rashin mutunci,kisan kai da ta'addanci. Don haka in zaku lura sosai zaku ga yadda suke kauce wa duk wata arangama ko yaki damu,domin sun sani sarai cewar 'duk wani yakin da zai barke nan gaba to lallai zamu karkare yakin ne a tsakiyar Tel-Aviv.




Yanzu haka ita kanta kasar Amurka ta rikice,kuma ta rasa abinda zatayi,tana cikin tsananin damuwa da tashin hankali. Don haka da sannu kowa zai ga wannan rana mai matukar muhimmanci garemu baki daya.
--------
Nasir Isa Ali



GA MASU BUQATAR SAMUN WASU RUBUTUKANMU TA WHATSAPP SU SHIGA LINK DIN DAKE QASA↧↧↧↧↧↧↧↧↧↧↧↧↧↧↧↧↧↧↧↧↧ https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

0 Response to "RIKICIN IRAN DA AMURKA---- AMURKA NA CIKIN FIRGICI SAKAMAKON JAWABIN SHUGABAN RUNDUNAR SOJAN IRAN AKAN QASAR ISLARA''ILA SHIGA DOMIN KARANTAWA"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?