--
Majalisar Tarayya Na Neman Dakatar Da Dokar Zarar Kudin Jama'a Da Bankin CBN Ya Fitar

Majalisar Tarayya Na Neman Dakatar Da Dokar Zarar Kudin Jama'a Da Bankin CBN Ya Fitar

Yunkurin da babbab bankin Nijeriya CBN ya zo da shi na zarar kudin masu ajiya ko kuma masu cira za ta zo karshe. Domin kuwa zauren majalisar Wakilai sun nemi CBN ya dakatar da wannan kudiri.

Benjamen Kalu daga jihar Abia shine wanda ya shigar da korafi a gaban majalisa.

Bayan shafe dogon lokaci Benjamen yana zabga Turanci, inda yake bayanin nuna rashin gamsuwa da wannan kudi, nan take sauran wadanda suke cikin zauren suka nuna goyon bayansu tare da amincews.

Ba tare da bata Lokaci ba, shugaban Majalisar ya amince da korafin Benjamen, wanda nan take ya rubutawa CBN sakon neman ya dakatar da wannan kuduri na cirar kudin jama'a.

Dama shugaban kasa ba shine yake da hakkin dakatar da CBN akan wannan kudiri ba.

Saboda CBN banki ne mai cikakken 'yancin aiwatarda duk aiki muddin zai kawowa tattalin arzikin kasa ci gaba. Saidai majalisa ba da damar hanawa.

0 Response to "Majalisar Tarayya Na Neman Dakatar Da Dokar Zarar Kudin Jama'a Da Bankin CBN Ya Fitar"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?