--
LABARAN MAKO----Manyan Labarai Da Suka Faru A Wannan Qasar Ta Nigeria Cikin Satin Nan

LABARAN MAKO----Manyan Labarai Da Suka Faru A Wannan Qasar Ta Nigeria Cikin Satin Nan

Rundunar 'yan sandan Jihar Neja ta kama mutane bakwai da take zargi da aikata kisan kai a cikin Jihar, rundunar tace ta kama Malama Harela Ubah wacce ake zargi da kashe diyar kishiyar ta, ta hanyar dura mata gubar "Piya Piya" a kauyen Shakodna dake karamar hukumar Shiroro, rundunar ta baiyana cewar " mijin matar mai suna Malam Ubah ne yakai rahoton faruwar lamarin a babban ofishin 'yan sanda dake yankin na Shiroro, inda yace " a lokacin da amaryar sa mai suna Khadija Ubah ta shiga makewayi domin yin wankan jego ta bar jinjirar 'yar kwana uku da haihuwa a daki lafiyar ta lau, bayan fitowar ta talura da wani farin kumfa na fitowa daga bakin yarinyar wanda hakan yasa sukayi gaugawar kaita asibitin gwamnati dake garin Kuta domin duba lafiyar ta inda likitoci suka tabbatar da guba aka bata wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar jaririyar.

Malam Ubah da mahaifiyar yarinyar sunyi zargin a lokacin da abun ya faru babu kowa a cikin gidan sai Harela, domin a lokacin da Malama Fa'iza (mahaifiyar yarinyar) ta shiga ban daki Harela kadai ta bari a cikin gida hakan yasa suke zargin ta da durawa jinjirar guba, bayan gudanar da bincike na 'yan sanda ga wacce ake zargin Herala ta amsa cewar kallai ita taba jaririyar 'yar kwana uku da haihuwa gubar "Piya Piya" wanda hakan yayi ajalinta.

A daya bangaren rundunar tayi nasarar kama wasu membobin kwamitin tsaro da gyaran tarbiyya wadanda ake yiwa lakabi da 'yan kwamiti da jami'an Hisba da laifin dukan wani matashi mai suna Ibrahim A. Ibrahim har lahira a garin Kontagora.

Rahotanni sun tabbatar da cewar 'yan kwamitin da jami'an Hisban da suka aikata wannan aika aikan sun kama mamacin ne bisa zargin sa  da suke yi da boye wata yarinya mai suna Maryam Salmanu a dakin sa dake Unguwar Yamma hakan yasa suka kamoshi da tare da wasu abokan sa guda biyu (Musa Salmanu da Ahmed Muhammad) inda sukayi masu dukan tsiyawa daga bisani suka saki abokan nasa biyu, ganin irin halin da yake ciki na jikkata suka kaishi dakin shi da daddare suka ajeshi ba tare da sanin 'yan uwan sa ba, iyayen sa sunyi kokarin kai shi asibiti domin duba lafiyar sa daga bisani rai yayi halinsa.

Rundunar 'yan sandar ta kara da cewar tana nan tana cigaba da gudanar da bincike akan wadanda take zargin, da zarar ta kammala zata gurfanar dasu gaban kotu.

Kwamishinan 'yan sandar Jihar Neja CP Usman Adamu yayi kira ga kungiyar sintiri na 'yan banga da 'yan sakai, da sauran kungiyoyin dake taimakawa domin yakar ta'addanci tare da gyaran tarbiyya da su cigaba da gudanar da ayyukan su bisa mutunta doka da oda tare da kare hakkin bil'adama.

CP Usman ya kara da cewar " Muna kara kira da neman goyon baya da hadin kan dukkan al'ummar Jihar Neja domin kawar da dukkan wani aikin ta'addanci da bata gari a cikin Jihar Neja, kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandar Jihar ta Neja Abubakar Dan Inna ya baiyana.

0 Response to "LABARAN MAKO----Manyan Labarai Da Suka Faru A Wannan Qasar Ta Nigeria Cikin Satin Nan "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?