--
Ina So Duk Wani Dan Siyasa Ya Yi Irin Siyasa Ta Na Tura 'Ya'yan Talakawa Karatu, Cewar Sanata Kwankwaso

Ina So Duk Wani Dan Siyasa Ya Yi Irin Siyasa Ta Na Tura 'Ya'yan Talakawa Karatu, Cewar Sanata Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Dakta Rabiu Musa Kwankwaso Yayin Da Yake Amsa Wata Tambaya Daga Yan Jarida Cewa Ya Gina Wata Makarantar Kwalejin Koyon Aikin Jinya Da Unguwarzoma A Garin Kwankwaso, Kuma Abokan Adawarsa Suna Cewa Ai Salon Neman Kudi Ne, Shi Kansa Wannan Tura Daliban Karatu Kasar Waje Da Yayi, Kawai Wayo Ne Domin Bukatar Siyasa A 2019.
Jagoran Kwankwasiyyar Yace "Ina Rokon Duk Wani Dan Siyasa Yayi Irin Wannan Siyasar, ya Gina makarantu ya tura matasa naiman Ilimi kyauta ,Ai Duk Wanda Yake Neman Kudi Da Ilimi Tabbas Mutumin Arziki Ne."

Sannan Ya ce Duk Bakin Cikin Masu Yi Masa Hassada Shidai Sai Ya yi Aikin Alheri, Kuma Yana Jan Hankalin Mutane Su Guji Kushe Aikin Alheri Koda Basa Kaunarsa, Saboda Cigaban Al'umma Ne, Kuma Ba Denawa Zaiyi Ba, Kuma Ya Kara Jan Hankali Akan Cewa Shima Fa Mutum Ne, Kawai Wata Dama na  Samu na  Waiwayi Baya Domin taimakon Rayuwar matasa.

Daga Umar Gaya

0 Response to "Ina So Duk Wani Dan Siyasa Ya Yi Irin Siyasa Ta Na Tura 'Ya'yan Talakawa Karatu, Cewar Sanata Kwankwaso"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?