--
AISHA BUHARI TA YI YAJI DAGA FADAR SHUGABAN KASA

AISHA BUHARI TA YI YAJI DAGA FADAR SHUGABAN KASA

Tana Ina? Mai Magana Da Yawunta Ya Sa Wa Bakinsa Takunkumi
 Tun Daga Aikin Hajji Har Yanzu Babu Labarinta
*Hadimanta Ne Ke Wakiltarta A Wajen Taro
*Tana Gudanar Da Harkokinta A Kafar Sada Zumunta
*Bincike Ya Nuna Tana Birnin Landan
*Tarihin Sukar Gwamnatin Mijinta

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta fice daga Nnajeriya kusan tsawon watanni biyu kenan zuwa yanzu, wanda hakan ya janyo kece-kuce a fadar Shugaban Kasa. Binciken jaridar Daily Trust daga majiya da dama ya tabbatar da cewa, Aisha Buhari ta yi yaji ne akan wasu dalilai. Kwakkwarar majiya ta ruwaito cewa matar Shugaban Kasa ta bar Najeriya ne farkon watan Agusta zuwa kasar Saudi Arabiyya domin aikin Hajji, daga nan kuma bata dawo kasar ba.

”Mama tana Landan. Daga kasar Saudi Arabiya ta wuce Landan” inji wata majiya. Da aka tambayi ko yaushe zata dawo, “Ban sani ba. Abinda kawai na sani tana Landan” An gane Mama bata nan ne a yayin da ba a ganta a wasu sha’anin mijinta ba.

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa ba a ga Aisha Buhari a shagalin bikin babbar Sallah da Buhari ya gudanar a garin Daura ba dake jihar Katsina. Haka zalika Shugaban Kasa ya karbi bakuncin manyan baki da dama da suka hada da Shugaban Kasar Guinea, Alpha Conde. Haka ma a kwanan nan Dr Hajjo Sani mataimakiyar Shugaban Kasa ta musamman a sha’anin mulki ce ta wakilici Aisha Buhari a wani taro. Ko a 25 ga Satumba Hajjo ce ta wakilce ta a taron matan Shugabannin kasashen Afirka da ya wakana a birnin New York na Amurka.

A cewar Daraktan yadda labaran Aisha Buhari ya ce, taron ya samu halartar matan Shugabannin kasashen Zimbabwe, Sierra Leone, Uganda da kuma Nijar, sannan Shugaban Kasa Mmuhammadu Buhari na daga cikin Shugabannin da suka halarci taron. Da aka duba shafinta na sada zumunta Twitter ya nuna tana ci gaba da gudanar da harkokinta domin ko a shafinta na Twitter @aishabuhari ta wallafa batun yaki da cin hanci da rashawa kwanaki shida da suka gabata.

Yunkurin jin ta bakin hadiminta a fannin yada labarai Suleiman Haruna ya ci tura, an aika masa da rubutaccen sako kamar haka: “Watanni kenan ba a ga motsin matar Shugaban Kasa ba a bainar jama’a, gida da kuma waje. A wasu sha’anin sai hadimanta ne ke wakiltar ta. Ina take?” Sau biyu ana aika masa wannan sakon. Kazalika an aikawa mai magana da yawun Shugaban Kasa Garba Shehu irin wannan sakon sai ya amsa da cewa, a tuntubi mai magana da yawunta.

SUKAR GWAMNATIN MIJINTA

Jaridar Daily Trsut ta ruwaito cewa, a Yunin wannan shekara, ta bayyana sauya sunanta daga Matar Shugaban Kasa zuwa First Lady. Har mijinta ya kammala wa’adin zangon mulkinsa na farko Matar Shugaban Kasa ake kiranta.

Ana rantsar da mijinta a zangon mulki na biyu ta yi kira da babbar murya akan rashin tsaro da ya addabi kasar nan. A yayin ziyarar ta garin Daura Aisha Buhari ta ayyana cewa, babban abin takaici ne ace mutanen da suka zabi mijinta da zuciya daya wasu tsageru su rika zubar da jinin su. Don dole a kyale mutane su fadi halin kuncin da suke ciki. Kuma idan jami’an tsaro ba su dauki mataki ba, kowa ma zai iya rasa ransa a hannun ‘yan bindiga. “ A lokacin da Sakataren Gwamnatin jihar Katsina ya shelanta abinda ke faruwa, sai na aikawa jami’an tsaro cewa, su kawo karshen wannan zubar da jinin ko kuma su bari duk a kashe mu. Don haka dole a kyale kowa ya bayyana kuncin da ya ke ciki”. Inji Aisha Buhari

Kwanaki hudu da rantsar da mijinta, a wani taro da ya gudana a fadar Shugaban kasa Aisha Buhari ta yi suka da kakkausar murya akan yadda aka fitar da zunzurutun kudade har Naira Biliyan Dari Hudu Da saba’in da digo takwas (N470.8bn) domin tallafawa marasa gata (SIP) amma babu abinda aka tsinanawa ‘yan Arewa da kudin.

Idan ba a manta ba ko a watan Oktobar 2016

0 Response to "AISHA BUHARI TA YI YAJI DAGA FADAR SHUGABAN KASA"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?