--
CIKKAKEN BAYANI AKAN YADDA AKE LEKEN ASIRINKA TA WAYAR SALULARKA SAIKU KARANTA SOSAI DOMIN MAGANCE MATSALAR DON GUDUN SATAR BAYANA NANKU!

CIKKAKEN BAYANI AKAN YADDA AKE LEKEN ASIRINKA TA WAYAR SALULARKA SAIKU KARANTA SOSAI DOMIN MAGANCE MATSALAR DON GUDUN SATAR BAYANA NANKU!

Rayuwa ayau ta ta'allaka akan wayoyin tafi da gidanka, kuma muna ganin wayar salula itace sirrin mu kuma ancikata da abubuwan nishadi, kamar waka, kallo, da kayan wasanni (Games), sannan tana dauke da mazubi na rayuwar yau da kullum (Knowledge Apps), dawainiyar rayuwa mafi yawa ayau ta koma waya, kama daga harkokin masarrafan taskar ajiya (Bank apps), da sauran abubuwa na rayuwa.
.

Alokacin da duniya take gaba, musamman ta fiskar kimiyya, bisa ga saukake harkoki, sai dankutse (Hacker) yake amfani da wannan dama wajen samar da abin nishadi ga wadannan wayoyi, domin amfanin mai waya yayi nishadi, yayinda shi kuma ta karkashin kasa yana samun baya nanka na wayarka, ta wannan salo ne yake amfani domin ya cimma burinsa na samun bayananka.kuma hanya ce mai sauki wajen samun duka wadannan bayanan naka, wato kamar lambobinka na sirri na banki, lambobin wayarka, sanin hakikaninka, duka ayau ga wanda yake amfani da android ba wuya bane asan inda yake.
1. LAUNIN MADANNAI (STYLE AND COLOUR KEYBOARD)
Wasu daga cikin masu amfani da android suna amfani da madannai na waya masu launi (Keyboard theme) wadanda wasu ba'ada sanin takamaiman wanda ya samar da su, hasalima kamfanin wayarka bashi ya samar da shi ba, kuma bai dora shi akan wayar amatsayin ka zabeshi idan kana bukatar launin kalar madannai ba, yayinda ka dauko irin wannan madanni daga yanar gizo ka sauko dashi wayarka,ya kamata kayi tunanin waya samar dashi, ya kamata ya zama ka karanta aikin da zaiyi akan wayarka, amma haka muke dora shi, zai tambayemu "Allow Keyboard to access your Contact" anan damar da ka bashi ita zata bashi dama ya yi amfani da lambobin wayarka,



Sannan yayinda kake shigar da bayananka na banki cikin (Application) na bankin da kake ajiya wannan madannin shi ne dai kake rubutu dashi. Abina "OK/Allow" kawai ka danna ya cire madannin da wayarka tazo dashi, shi ya maye gurbin na wayarka shi ne bazai iya daukar duk abinda kake latsawa ya kaiwa mai gidansa ba? akwai launin keyboard wanda waya take zuwa dashi, ayau idan ka sayi sabuwar wayar kamar "tecno tana zuwa da Swiftkey" kuma acikinsa yana zuwa da launin madannai kala-kala, wanda komai ya faru ta silar madannai kana iya kaiwa kamfanin wayarka kara kotu, kuma duka wayoyin yanzu wasu suna zuwa da nasu daga kamfani kai tsaye.

.





2. SALO DA LAUNIN CIKIN WAYA
Akan samu "application" wanda shi launin cikin waya yake canzawa, misali kamar rubutu ya zama manya (Bold) ko ya canza su zuwa kwantattu (Italic), irin wannan "application" ya kamata ya zama cewar kasan inda ya fito kafin fara amfani dashi,domin zai iya nadar duk abinda yake wayarka na bayani ya kaiwa mai shi ya kamata muyi nazari akan wannan.



3.BAWA APPLICATION DAMAR KARANTA LAMBOBIN WAYA (ALLOW APP TO ACCESS YOUR CONTACT)
Yayinda kake kokarin bude wani "application" akan android dinka, shi kuma wannan "application" yake bukatar karanta lambobinka domin gudar da aikinsa, to ya kamata ka tsaya ka nutsu kafin fara amfani dashi, sannan ya kamata ka samu cikakken bayani akansa, domin duk "application" din daya bukaci amfani da llambobin wayarka, to yana iya amfani da wannan dama, ya damfari abokan huldarka,ta hanyar kiransu awaya ko tura sako,



Da bukatar wani abu agaresu, ko kuma amfani da bin diddigin su ta hanyar shigo da lambobinsu zaurukan sada zumunta, yana daga cikin hanyoyin da ake samun damar turowa mutanemmu sako, da cewar daga banki, domin a damfaresu, wadanda suke bude facebook da lambar waya ana amfani da wannan salon domin akarbi account na wani, acanza sunansa zuwa na wani daban.matukar kana amfani da "application" irin wadannan to baka  da kariya cikin abokan huldarka, sannan baka basu wata kariya ba.

.


4. SANIN INDA KAKE ( ALLOW APP TO ACCESS YOUR LOCATION)

Mafi yawan masu amfani da waya kirar android suna samun wani "application" acikinta mai suna "Palmchat" wannan "application" yayi kyau kuma yana da dadin sha'ani, amma babbar matsalar daya samu yadda yake bayyana inda masu yinsa suke, wannan tsarin ya samar masa da matsala babba ta rashin samun yawan mabiya, hakan ya biyo bayan nuna muhimmancin boye wurin da kake domin gudun sata, damfara ko "Kidnapp" wanda ya zama ruwan dare, amma sai kaga mutum ya dauko "application" kana budeshi yace yana bukatar sanin inda kake domin ya fara aikinsa, saika ce wanda zai baka bashin kudi, saiya san inda kake, irin wadannan "application" ya kamata musan wanda zamuyi amfani dasu, domin ka guje samun matsala akanka ko a iyalanka ko a yan uwanka. bawa "application" damar yasan inda kake wannan babbar matsala ce, ya kamata kasan irin wadanda zaka ba wannan damar, bawai kawai daka dauko abu a yanar gizo zaka amince masa ba, za'a iya amfani da wurin da kake a damfareka ko waninka.




5. SAMUWAR HOTONKA ASAUKAKE KODA BAKA FACEBOOK (ALLOW APP TO ACCESS YOUR CAMERA)

Camera abace wacce take da kima a duniyar android ayau, sannan tana daya daga cikin hanyar samun cikakken bayanin siffarka ta hanyar CAMERA ta gaba (Front Camera/ selfie camera) da wannan abar daukar taswirarka ta gaba za'a iya samun hotonka, abin lura anan shi ne, kana iya dauko application kuma ya bukaci amfani da camera ta wayarka kafin ya fara amfani, irin wadannan application abin lura shi ne waya samar da su, sannan wanne aiki zasu yi maka da dole suke bukatar amfani da Camera ta wayarka kafin fara aikinsu, ya kamata kayi nazarin application kafin bashi dama yayi amfani da Camera a wayarka,


Domin wanda ya samar dashi zai iya cutar da kai ko waninka, misali ka dauko "Anti theft" kasa shi a wayarka mai security, kaba wani ya bude key din wayarka ko kuma ka ajiyeta agida, duk wanda ya dauka yayi kokarin cire wannan key, matukar bai iya ba, kana budeta kai mai ita, hoton duk wanda yasa key ko pattern ba dai-dai ba zaka ganshi akan wayarka, shi to shi wancan application daka sa kasan adadin hoton mutum nawa ya dauka, sannan mutum nawa zai cutar, ba lallai saikai zai cutar ba, yana iya cutar da wani naka.


.

6. RASHIN SIRRI WAJEN KIRAN WAYA

Duk wanda ya kwana ya tashi yasan cewar kamfanin da suka samar da layin wayarsa suna ajiye da duk wata shira da yayi ta wannan waya, cin zarafi, zance da budurwa, zancen ta'addanci kona masalaha, duk wadannan kamfanin layinka suna ajiye dashi, bayan wancan sai kuma wani can baka sanshi ba, kana magana yana datsar mai kake cewa, ta hanyar saukar da application dinsa da kayi cikin wayarka,misali kamar "True Caller" mafi yawa daga masu amfani dashi yana ajiye musu sautin muryarsu, kuma suna jin dadi, amma abinda basu sani ba shi ne,


Shima yana da bayanaka cikin datarsa, amma gara shi,  tunda zaka iya kaishi kara kuma a bibiyi masu shi tunda ansan masu shi a duniyar kimiyya, amma wasu wadanda ba'a san waya samar dashi ba wannan akwai matsala, domin ana iya amfani da wannan damar tunda ya nadi sautin muryarka, sannan ya samu lambobinku da kai da wanda kake yiwa waya. Idan kai da ka saukar dashi mai cutar da kaiba, saiya cutar da wanda kake hulda dasu.kana iya yin sila acutar da abokinka wanda yake wata kasar, ta silar waya da yayi da kai.



7. BA KAI KADAI KAKE KARANTA SAKONNINKA BA (USE APP AS YOUR DEFAULT SMS)

Sakon wayarka ma kace saika yi amfani da wani app wajen ajiyesu da karantasu, anan bai kamata ace bangaren sako sai kayi amfani da wani application ba, misali kamar "True caller" yana karanta sako, idan kayi kokarin goge sako awaya, ko kuma ka bude shi ka karanta, amma kaga alamar sa bata canza ta cewar anbude shi ba, to kana amfani da apps mai karanta sako, domin ba kowanne lokaci yake baka dama ka iya goge sako ba da kanka, idan ka samu kanka a irin wannan matsala saika bude  Message> SMS Setting> SMS Disable saika latsa wurin zai dawo maka da asalin naka nan take zai baka dama ka goge sako kai tsaye.saka irin wadannan abubuwa suna haifar da matsala, domin suna karanta duk sakon shige-da-fice na kudi da kake yi a bankin ka, sannan zasu samu wani sakon na kasuwanci, koda sakonka na Whatsapp irin wadannan apps suna karantawa, tunda ka basu dama.
.




8. KAYAN NISHADI (GAMES)

Game yana daya daga cikin abinda yasa mutanen mu suke siyan waya kirar android, abin lura anan akwai game mai bukatar amfani da wasu sassa na wayarka kafin ya fara aikinsa, kamar game yace yana son yasan inda kake (Access Location), ko kuma yana bukatar amfani da bangaren sako, domin sanar maka da abinda kayi (SCORE), koya bukaci amfani da Camera idan kakai wani mataki, atakaice ba duk Game ne mai bukatar Network yake mai kyau ba, kuma yake mai tsaro ba, zaifi kyau idan zakayi Game a wayarka ya zama ka rufe "Data" dinka, karma ya samu damar amfani da wannan ya tura wasu abubuwan daya samu akan wayarka zuwa ga mai gidansa.

.
9. APPLICATION MASU ALAKA
Wani yana yin facebook, sai yace lallai yana bukatar yin rubutu manya cikin "Bold Post" da zai gabatar ko kuma yana son yayi rubutu akwance (Italic) amma babu tsarin a facebook, akokarinka na lallai sai kayi wannan rubutu saika, shiga binciken ya zakayi, saika fada google acan zaka samo application wanda wani ya samar domin aiki irin wannan tunda dama yasan za'a zo nemansa, kana sauko dashi zai bukaci ka shigar da bayananka na facebook, kana shigarwa shi kuma wanda ya samar dashi zaiyi amfani da wannan dama ya shiga facebook dinka,

Yayi duk abinda yake so, yana iya bukatar kudi awajen wasu wadanda kake hulda dasu ta kima, ko kuma yayi ta turo maka da hoton batsa cikin "timeline " dinka, ka rasa waye yake masa post na batsa ko ya canza maka suna a facebook dinka. ta wannan hanyar shi wannan application din yana iya amfani da duka bayananka na cikin waya, ta wannan salon wanda ya samar da application din zai iya cutar da kai.


Idan ka kasance kana bukatar amfani da wani salo a zauren sada zumunta kamar facebook, twitter, ko Whatsapp, ka fara duba bangaren taimakon su na gaggawa, ka tambayesu, idan salon sun samar dashi zasu baka bayaninsa, amma idan basu baka shi ba to wannan tsarin da salon babushi a salon su.saboda haka hakuri da jiran lokaci shi ne mafita, kai gara ku tura musu "Report" akan kuna bukatar tsari kaza saisu duba yiwuwarsa.



.
Akwai Application masu bukatar duka wadannan abubuwan dana lissafo, kamar True caller shi kadai yana amfani da duka abubuwan dana zayyano daga 1 zuwa 7, sannan akwai application masu bukatar wadannan abubuwa, dole mu zama masu lura akansu da yadda zamu kare kammu daga garesu. domin kata wannan hanya zamu cutu ko mu cutar da wasummu, karka dauka kai kasan waya, baza'a cutar da kaiba, ko ka cika baki akan baza'a cutar da kaiba, sai ayi amfani da kai acutar da waninka. ya kamata mu rika duba gudanarwar apps na wayoyinmu, kana iya kashe shi ko ka kunna (ON/OFF APPS PERMISSION) koda a google play zaka dauko apps ya kamata ka duba abinda zai bukata akan wayarka kafin sauko da shi

MUNA ALFAHARI DAKU MASU BIBIYAR WANNAN SHAFI MUNA GODIYA DA KASANCEWARKU GAREMU MUNA FATAN ZAKU TAYAMU YADA WANNAN SHAFI NAMU DOMIN SAURAN AL-UMMAH SU GANI KUMA SU AMFANA MUNA QARA SANAR DAKU CEWA MUNA SIYAR DA DATA TA KOWANE KAMFANI A NIGERIA MTN DATA, AIRTEL DATA, 9MOBILE DATA GLO DATA, GAMAI BUQATA YA KIRAMU TA NUMBOBIN WAYA KAMAR HAKA 08133888333, 09066633320, MUNGODE!!!


DOMIN SAMUN WASU RUBUTUTTUKAN NAMU TA WHATSAPP GROUP KU DAN WANNAN LINK DIN DAKE QASA DOMIN SHIGA YANZU ↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓
                                                                                                         https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

0 Response to "CIKKAKEN BAYANI AKAN YADDA AKE LEKEN ASIRINKA TA WAYAR SALULARKA SAIKU KARANTA SOSAI DOMIN MAGANCE MATSALAR DON GUDUN SATAR BAYANA NANKU!"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?