--
Shin wani zai iya amfani da BVN ya satar min kudi a Banki na?

Shin wani zai iya amfani da BVN ya satar min kudi a Banki na?

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suke yawan yi a lokacin da kamfanoni ko ma’aikatu suka nemi mutum ya bayar da lambobin BVN din sa, Kafin mu bayar da wannan amsar, da farko dai ya kamata mu fara tambayar kanmu shin wai menene BVN?
BVN na nufin Bank Verification Number wato waɗansu lambobi da banki suke baiwa kowane mutum bayan sun karɓi waɗansu bayanai daga gare ka wanda ya kun shi, cikakken sunanka, da adireshinka, da lambar wayarka da hoton fuskarka, da hotunan ‘yan yatsunka.
Wannan shine BVN kuma makasudin yin sa shine domin tabbatar da tsare dukiyar jama’a da tantance adadin jama’ar da suke yin mu’amala da bankuna a kowace kasa.
Bayan banki sun karɓi wannan bayanai duk wani asusun ajiyar kudi da zaka bude a kowane banki ba sai kasake bayar da bayanan ka ba, kana basu wannan lambar shike nan suna da komai naka.

Sai mu koma ga amsar tambayar mu na cewar Shin ana iya satar kudin mutum ta amfani da BVN? Wannan maganar kwata-kwata ba gaskiya bace, babu alaka da tsakanin BVN da Account number din ka ta wurin cire kudi. Domin da za ka je banki cire kudi sai ka manta ka rubuta BVN dinka a takardar karbar kudi, mai biya ba zai iya sanin account dinka ba.
Akwai banbanci tsakanin BVN da PIN number dake jikin ATM dinka, wanda shi PIN din ATM shike da hatsari sosai wurin fadawa hannun miyagun mutane.
Amma duk da haka ba mu ce koina ka saki BVN dinka ba.
GAMAI tambaya ko qarin bayani yayi aqasan Rubutun nan 👇👇👇

1 Response to "Shin wani zai iya amfani da BVN ya satar min kudi a Banki na?"

Tell us what you think about this article?